Jamb-ta-janye-bukatar-katin-dan-kasa-jarabawar-bana

A Najeriya hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu da ake kira JAMB ta janye kudirin hana duk wani dalibi da ba shi da lambar katin shaidar dan kasa ta NIN sukunin sayen fom din za na jarabawar don neman gurbi a manyan makarantun kasar.

Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede, da ke tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja babban birnin Najeriyar, ya ce a wanna karon hukumar za ta daga kafa don bai wa dalibai damar mallakar katin shaidar dan kasar kafin badi.

Acewar Oloyede matakin na da nasaba da tangardar na’urar da hukumar samar da katin dan kasar ta samu da ya hana gudanar da aikin cikin hanzari.

Sai dai shugaban na hukumar JAMB ya ce rijistar jarabawar ta JAMB a shekara mai zuwa ta 2021 zai zama dole sai da bayanan katin dan kasar ga kowanne dalibi da ke Najeriyar.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *