Iran-ta-amsa-laifin-harbo-jirgin-ukraine-bisa-kuskure

Bayan share dan gajeren lokaci ana caccar baka dangane da batun harbor jirgin fasijan Ukraine aTehran, kasar Iran ta amsa cewa bisa kuskure ne rundunar tsaron kasar ta kakkabo jirgin fasinjan kasar Ukraine yan lokuta da cirawar sa daga filin tashi dama saukar jiragen saman birnin Tehran.

Kasashen Canada da Ukraine sun bukaci a gurfanar da sojojin dake da hannu a batun harbo jirgin fasijan Ukraine tareda samar da hanyoyin biyan diya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukan su .

Mutane 176 ne suka rasa rayukan a wannan hatsari da ya hauku a Tehran.

Ministan harakokin wajen kasar ta Iran Javad Zarif ya roki iyalen mamatan, tareda neman gafarar jama’a biyo bayan wannan kuskure.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *