Yan-gudun-hijira-nijar-sun-kone-rumfunan-sansaninsu-da-ke-agadez

Wani gungun ‘yan gudun hijira wadanda suka samu mafaka a jihar Agadez da ke Jamhuryar Nijar, sun kone rumfunan da aka kafa a sansaninsu da ke yammacin garin na Agadez.‘Yan gudun hijirar sun kona sansanin ne bayan shafe kwanaki suna zaman dirshin a gaban offishin hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR. Tuni jami’an tsaro suka kame akalla 100 daga cikinsu wadanda ake zargi da haddasa gobarar. Daga Agadez ga rahoton Omar Sani.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *