Jamhuriyar-benin-ta-kaddamar-da-wani-gagarumin-shirin-tantance-yan-kasar-najeriya

Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta kaddamar da wani gagarumin shirin tantance ‘yan kasar da ke zaune a tarayyar Najeriya.

Da jimawa dai ne Jamhuriyar Benin ta shirya gudanar da wannan aiki,wanda zai taimaka don tattance yan kasar ta dake zaune waje tareda basu damar  gudanar da harakokin su a tsanake.

Benoua Adekambi, mai bai wa ministan harkokin wajen kasar ta Benin shawara ya bayyana cewa babbar manufar wannan shiri ita ce tantance illahirin ‘yan kasar Benin da ke zaune a Najeriya. Abin tuni a nan shi ne, yau kimanin shekara daya da rabi kenan da aka kaddamar da irin wannan aiki a cikin gida Jamhuriyar Benin.


Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *