Sanya-dokar-ta-baci-iraki-bayan-mutuwar-mutane-13

Hukumomi a Iraki sun bayyana sanya dokar takaita walwala a Nasiriyah dake kudancin kasa a Alhamis, bayan harbe mutane 13 har lahira a diran mikiyar da jami’an tsaro suka yi wa masu zanga –zangar kin jinin gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa an girke jami’an tsaro ko ina a gefen birnin, inda suke binciken duk wani abin hawa dake kokarin shiga birnin.

Wannan ya biyo bayan sanya dokar ta – baci ne a birnin mai tsarki na Najaf, bayan damasu zanga – zanga suka banka wa ofishin jakadancin Irandake yankin wuta cikin dare.

Firaministan Iraki dayarasa tagomashin sa, Adel Abdel Mahdi ya aike damaanyan kwamandojin soji da dama zuwa lardunan dazanga – zangar ta yi kamari.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *