Bolivia-ta-nada-jakada-zuwa-amurka

Gwamnatin rikon kwarya a Bolivia, ta nada jakada zuwa Amurka karon farko a cikin shekaru 11.

Wannan dai wata alama ce ta samun kusanci tsakanin Amurka da Bolivia, bayan da rikicin siyasa ya tilasta wa Evo Molares yin marabus daga mukaminsa makonni biyu da suka gabata.

Makonni biyu da suka gabata ne wakiliya a Majalisar Dattawan Bolivia ta sanar da itace sabuwar shugaban kasar bayan da Evo Morales ya ajiye shugabancin ya tsere zuwa Mexico don samun mafakar siyasa.

Jeanine Anes daga bangaren adawa ta sanar da cewa ita take kan layi a jerin masu hawa kujeran kuma za ta ci gaba da tafiyar da mulkin kasar.

Tsohon shugaba Evo Morales ya soki nadin da wakilar majalisar Dattawan ta yi cewa itace sabuwar shugaban kasar.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *