Shugaban-kasa-ya-yi-murabus-saboda-zanga-zanga

Shugaban Bolivia, Evo Morales ya yi murabus daga kujerarsa bayan zanga-zangar makwanni uku da aka gudanar ta nuna adawa da sake zaben sa a karo na hudu, yayin da sojoji da ‘yan sandan kasar suka juya masa baya.

Dandazaon jama’a ya bige da murna a kan titunan La Paz jim kadan da sanar da murabus din Morales wanda ya kasance shugaban kasa mai ci mafi dadewa kan karaga a yankin Latin Amurka.

A yayin bikin murnar kawo karshen mulkinsa, jama’ar kasar sun yi ta yin wasan tarsatsin wuta tare da daga tutar kasar sama mai launin ja da shudi da kuma kore.

Madugun ‘yan adawar kasar wanda ya kara da Morales a zaben watan Oktoba, Carlos Mesa, ya bayana cewa, Bolivia ta koya wa duniya darasi, yana mai cewa kasar za ta zama tamkar sabuwa.

Wata tawagar kwararrun jami’an tantancewa daga Amurka ce ta gano cewa, an tafka gagrumin kuskure a zaben na watan Oktoba, lamarin da ya diga ayar tambaya kan sahihancin nasarar Morales.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *