Kwallon-kafa-najeriya-ta-sha-kashi-wasan-neman-olympics

Ivory coast ta doke Najeriya da ci daya mai ban haushi a gasar matasa ta ‘yan kasa da shekaru 23, inda ake fafutukar neman tikitin shiga gasar kwallon kafa ta Olamfik da zata gudana a birnin Tokyo na Japan, wasan farko na ruknuni na 2 da aka fafata a birnin Alkahira na kasar Masar.

Silas Gnaka ne ya saka kwallo a ragar Najeriya daga bugun – daga – kai – sai – mai- tsaron – raga, bayan wata rafka da dan wasan baya, Olisa Ndah ya yi, lamarin da ya kai ga ba shi jan kati saura minti 20 a tashi wasa.

Bayan wannan wasa ne fa aka barje gumi tsakanin Afrika ta kudu da Zambia, inda aka yi canjaras 0-0, ba kare – bin damo a filin wasa na Al Salam.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *