Ba-zan-yi-biris-da-bayern-munich-ba-wenger

Tsohon mai horar da’yan wasa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya yi bayanin yadda yake sha’awar kugiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, abin da ke dada sa wa ake tunanin zai yi aiki da kungiyar.

Arsene Wenger bai ce ba zai horar da kungiyar ba idan ya samu dama, biyo bayan rahotannin da ke cewa yana hanyarsa ta zuwa kungiyar tun da ta sallami Niko Kovac.

Dan shekara 70 din bai samu aikin horar da wata kungiya ba tun da ya yi hannun riga da Arsenal a kakar wasanni ta 2018, amma ya sha zakewa cewa yana da sha’awar komawa aikin horar da’yan wasan tamaula.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *