Madrid-za-ta-bayar-da-bale-domin-sayo-sterling

Real Madrid na shirin mika dan wasanta na gaba, Gareth Bale tare da karin Pam miliyan 70 domin Manchester City ta ba ta Raheem Sterling.

Sky Sports ta rawaito cewa, wakilan Real Madrid za su yi balaguro domin kallon bajintar Sterling a wasan da kasarsa ta Ingila za ta yi a watan gobe a gida da Montenegro da kuma wanda za ta yi a waje da Kosovo, kafin daga bisani su tsayar da shawarar mika bukatarsu ga Manchester City.

Rahotanni sun tabbatar cewa, Sterling na shaukin taka leda a gasar La Liga ta Spain.

To sai dai wani kalubale da wannan cinikayyar ka iya fuskanta, shi ne Manchester City musamman ma kocinta, Pep Guardiola ba shi da sha’awar daukar Bale mai shekaru 30.

Kazalika muddin Bale ya zabi ci gaba da zama a Real Madrid, hakan zai tilasta wa kungiyar lale kimanin zunzurutun Pam miliyan 200 a matsayin farashin Sterling, wato kwatankwacin kudin da Barcelona ta karba daga PSG domin sayar da Neyma.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *