Hare-haren-yan-taadda-sun-tsananta-yankin-sahel

‘Yan ta’adda sun sake kaddamar da wani sabon farmaki a Burkina Faso,inda suka kashe jami’an tsaro biyar,  harin da ke zuwa a daidai lokacin da ake zaman makoki a Mali biyo bayan kisan da ‘yan ta’ddan suka yi wa sojojin kasar kimanin 50.

Kazakila mayakan masu ikirarin jihadi sun kai makamancin wannan harin Jancinsa a jamhuriyar Nijar, inda suka hallaka sojojin kasar 12, lamarin da ya sa ake diga ayar tambaya dangane da amfani ko rashin amfanin dubban dakarun kasashen Yammacin Duniya da ke jibge a cikin wadannan kasashe na yankin Sahel.

Ko a Najeriya, mayakan sun sha kaddamar da irin wannan farmakin kan jami’an tsaro musamman a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikicin Boko Haram.

A yayin zantawa da sashen hausa na RFI, Alkassoum Abdourahman mai sharhi kan lamurran yau da kullum a Jamhuriyar Nijar, ya ce, muddin ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, wasu yankuna za su bukaci ballewa daga wadannan kasashe domin cin gashin kansu.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi da Alkassoum Abdourrahman.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *