Muna-iya-kaurace-wa-wasan-carabao-klopp

Mai horar da ‘yan wasan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce kungiyar na iya kaurace wa wasan daf – da – na – kusa – da karshe a gasar kofin Carabao har sai an sanya wasan a lokacin da ya dace.

Liverpool ta samu zuwa wannan mataki na quarter finals ne bayan sau biyu ta taso daga baya ta farke kwallayen da Arsenal ta saka a ragarta lamarin da ya sa wasa ya kare canjaras 5-5 bayan mintuna 90, sannan ta doke Arsenal din a bugun fenariti.

Hukumar kula da gasar League ta kasar Ingila dai na shirin sanya wasannin daf – da – na – kusa – da – karshe a ranar 16 ga watan Disamba, kuma a ranar 18 ga watan Disamba ce Liverpool za ta fafata a wasan kusa da karshe na gasar kofin kungiyoyin duniya.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *