Bankin-duniya-zai-zuba-jari-don-farfado-da-tafkin-chadi

Bankin duniya ya sanar da aniyar zuba jarin dala miliyan 510, domin raya yankin tafkin Chadi, don magance matsalar tsaro da kwararowar hamada da kuma matsalolin jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta yanzu haka.

Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed wadda ke sanar da matakin na Bankin Duniya yayin wani taron manema labarai a Washington DC na kasar Amurka, a gefen babban taron asusun bada lamuni na duniya IMF tare da hadin gwiwar Bankin ta ce akwai fatan matakin ya tallafawa wajen samar da tarin gurabe aiki baya ga bunkasa tattalin arzikin yankin.

A cewar Zainab Ahmed bankin zai zuba kudaden ne a kashi 3 bangare daban-daban cikin kasashen da ke kewaye da tafkin na Chadi da suka kunshi  Najeriya, Nijar, Kamaru da kuma Chadi.

Ministar kudin ta Najeriya ta ce kason farko na kudin na dauke da dala miliyan 170, don magance wasu matsalolin da kasashen yankin ke fama yanzu haka masamman tsaro.

Zainab Ahmed ta kuma bayyana cewa za a yi amfani da wani bangaren kudin wajen ayyukan gina-gine da hanyoyi da zai sada kasashen hudu, za kuma a bayar da tallafi ga al’ummomin da ke rayuwa a yankin don inganta juriyarsu, kana da samar da ababen more rayuwar jama’ar yankin.

A bangare daya ministar ta kuma bayyana cewa, Gwamnatin Tarayyar Najeriya na shirin kara rancen kudi daga bankin na duniya na dala biliyan 1 kan biliyan 3 da ta karba tun farko domin inganta wutan lantarki.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *