Yunwa-ta-hallaka-giwaye-55-gandun-dajin-zimbabwe

Akalla Giwaye 55 suka mutu a Zimbabwe sakamakon tsananin farin da ya afkawa kasar, wanda ya haifar da rashin abinci da ruwan sha.

Kakakin hukumar kula da gandun dajin kasar, Tinashe Farawo ya ce daga watan Satuma zuwa yanzu, giwaye 55 suka mutu a Gandun Dajin Hwange.

Jami’in ya ce anyi gandun dajin ne domin aje giwaye 15,000, amma yanzu haka suna da giwayen da suka zarce 50,000.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan kashi daya bisa uku na al’ummar Zimbabwe, wato mutane sama da miliyan 5 ke fuskantar barazanar karancin abinci kafin lokacin girbin da za’ayi a shekarar mai zuwa.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *