Trump-na-son-jamiyyarsa-ta-republican-ta-tseratar-da-shi-daga-tsigewa

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci Yan Jam’iyyar sa ta Republican da su tashi tsaye domin kare shi daga barazanar tsige shi da Majalisar wakilai keyi, inda yake cewa Majalisar na daukar matakan gaggawa wajen raba shi da kujerar sa.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin taron Majalisar ministocin sa, yayin da ‘yan Jam’iyyar Democrats ke cigaba da samun goyan bayan jama’a a cigaba da binciken da su ke gudanarwa.

Shugabar Majalisar Nancy Pelosi ta gabatar da wani bidiyo mai dauke da shaidun da su ke amfani da shi wajen tsige shugaban saboda amfani da ikon sa ta hanyar da bata kamata ba, da suka hada da matsalar Ukraine.

A watan jiya shugaba Trump ya ce ko gezau baya yi dangane da yunkurin tsige shi, yayin da daga bisani ya kuma ce idan aka tsige shi, za’ayi yakin basasa a Amurka.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *