Putin-zai-karbi-bakoncin-shugabannin-afrika-45-taronsu-da-rasha

Shugaban Rasha Vladmir Putin na shirin karbar bakwancin shugabannin kasashen Africa, a wani taron karfafa dankon zumunci tsakanin Nahiyar da Moscow irinsa na farko a tarihi, taron da ake sa ran Rashan ta alkawarta taimakawa kasashen ta hanyar basu gudunmawa ba tare da gindaya sharudda kwatankwacin na kasashen yammaci ba.

Sanarwar da fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ta fitar ta ce akalla shugabannin kasashen Africa 47 ake dakon isarsu garin Sochi wajen da taron zai gudana wanda za a fara tsakanin ranakun gobe Laraba da jibi Alhamis.

Tuni dai Rashan ta bayyana alfahari da yadda kasashen na Afrika suka amsa goron gayyatarta zuwa taron wanda ke da nufin karfafa dankon zumunci tsakanin kasar da nahiyar ta fuskar kasuwanci, siyasa, tsaro da kuma bunkasa ci gaba.

Africa wadda ke da kasashe 54 a hukumance ana ganin za ta ci moriyar alakar da Rasha wadda ke matsayin kasa mafi noma da kuma fitar da alkama a duniya baki daya baya ga kaurin sunanta ta fuskar samar da makamai.

A bangare guda itama Rashan alakar za ta bunkasa kasuwancinta musamman ta fuskar takin zamaninta dai dai lokacin da manyan kasashen Afrikan ke kokarin karkata kasuwancinsu zuwa fannin noma.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *