Taron-samar-da-kudi-don-yakar-cututuka-duniya

Yau laraba aka fara taron kasa da kasa a birnin Lyon na kasar Faransa, domin tara dala bilyan 14 da zasu taimaka wajen yakar cutar HIV, zazzabin cizon sauro da kuma babban tari, da ke matsayin manyan cututukan da suka fi addabar jama’a a Duniya.

Daya daga cikin kwarraru mai suna Dr Habimana Phanuel, shugaban ofishin hukumar lafiya ta duniya a yankin tsakiyar Afirka, ya ce suna da kyakkaywan fata a game da taron.

Dokta Habimana ya na mai cewa “Abin da ya kamata a lura a nan shi ne, wadannan cututuka ne suka fi yin kisa a wannan zamani, saboda haka ya zama dole kasashe su yunkuro tare da samar da kudaden da za yi amfani da su domin yaki da su”.

A Afirka,wani bincike ya na nuna cewa wadannan cuttutuka na kashe milyoyin mutane a kowace rana tare da kasancewa babban tarnaki ga cigaban wadannan kasashe.

A gaskiya a cewar jami’in akwai su da kwarin gwiwar dangane da wannan taro,zai yi nasarar tara makudan kudade da za a yi amfani da su domin taimaka wa kasashen da wadannan cututuka da suka kasance barrazana.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *