Tsamo-gawar-yan-cirani-13-gab-da-tsibirin-lampedusa

Jami’an tsaron gabar teku a Italiya sun tabbatar da tsamo gawar wasu ‘yan cirani 13 ciki har da mata masu ciki 2 bayan kifewar jirginsu mai dauke da mutane 50 gab da tsibirin Lampedusa.

Rahotanni sun bayyana cewa kawo yanzu ana ci gaba da neman gomman ‘yan ciranin ciki har da kananan yara 8 da suka nutse a ruwan.

Da safiyar yau ne jami’an tsaron gabar tekun suka ceto mutane 22 da ransu yayinda su ke ci gaba da laluben wadanda suka bace.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *