Yan-sandan-najeriya-sun-bankado-maaikatar-sayar-da-jarirai-lagos

‘Yan Sanda a birnin Lagos da ke Najeriya sun sanar da kubutar da wasu ‘Yan mata 19 dauke da ciki a wani gida da ake sayar da jarirai da ke unguwar Ikotun, inda suka kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu wajen aje su.

Mai Magana da yawun rundunar Bala Elkana ya shaidawa manema labarai cewar DPO’n da ke kula da tashar ‘yan Sandan Isheri-Osun, Chike Ibe ne ya jagoranci aikin bankado gidan, inda aka samu ‘yan matan dauke da juna biyu.

Sanarwar ‘Yan Sandan ta ce ‘yan matan da suka fito daga Jihohin Rivers da Cross River da Akwa Ibom da Anambra da Abia da kuma Imo sun yi zargin cewar ana kama su ne a musu fyade, kuma idan sun samu ciki, sai a tsare su har sai sun haihu domin a sayar da jariran.

Rundunar Yan Sandan ta ce yanzu haka tana tsare da Happiness Ukwuoma da Sharifat Ipeya da ake zargin suna kula da gidan, yayinda shugabar su Madam Oluchi ta yi batar dabo.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *