Shugabannin-kasashen-duniya-za-su-karrama-chirac-paris

Ana sa ran shugabannin kasashen duniya da dama da suka hada da Vladimir Putin na Rasha su halarci birnin Paris a wannan Litinin domin karrawama ta karshe ga marigayi tsohon shugaban Faransa, Jacques Chirac wanda al’ummar kasar ke zaman makokin mutuwarsa.

Shugaba Putin da sauran shugabannin na kasashen duniya da mai masaukin baki, wato shugaba Emmanuel Macron, za su yi wa marigayin addu’a a Majami’ar birnin Paris, kuma hakan na zuwa ne bayan kwana guda da dubban jama’ar kasar suka yi dogon layi domin yi wa akwatin gawar Chirac ganin karshe.

Shugaba Putin da Firaministan Hungary Viktor Orban da shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da sauran shugabannin da suka yi aiki da Chirac za su kasance a wannan karramawa, sai dai Sarki Mohammed na 6 na Morroco ba zai samu damar hallara ba duk da kusancin da ke tsakaninsa da marigayin.

Chirac wanda ya mutu a  ranar Alhamis da ta gabata yana da shekaru 86,ya sha jinjina da yabo daga sassan duniya musamman saboda jajircewa da kwarjininsa a zamanin da yake kan ganiyar siyasa.

A yayin wani jawabi ga Faransawa, shugaba Macron ya bayyana marigayi Chirac a matsayin gwarzon jarumin da ya daukaka darajar Faransa a idon duniya.

Chirac ya shafe shekaru 30 yana siyasa, inda  ya yi shugaban kasa na shekaru 12, daga 1995 zuwa 2007.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *