Pakistan-ta-gargadi-mdd-kan-kazancewar-rikicinta-da-indiya

Fira Ministan Pakistan Imran Khan ya gargadi majalisar dinkin duniya da cewar rikicin dake tsakaninsu da Indiya kan yankin Kashmir, ka iya kazancewa zuwa barkewar yaki da makaman nukiliya, abinda ba zai yiwa duniya dadi ba.

Imran Khan ya yi gargadin ne a lokacin jawabi a zauren majalisar dinkin duniya, dake ci gaba da taron ta kashi na 74.

Fira Ministan na Pakistan yace yanzu haka India ta jibge jami’an tsaro dubu 900,000, a yankin Kashmir mai rinjayen Musulmi dake karkashinta, matakin da ake ganin zai sa su arangama da mutanen Yankin wadanda ke cikin ukubar rashin walwala yanzu haka.

Rikici ya so barkewa a yankin na Kashmir ne, bayan da Indiya ta soke kwarya-kwaryar ‘yancin da yankin na Kashmir dake karkashin ta ke da shi, bisa zargin cewa Pakistan kan amfani da yankin wajen kaddamar da ayyukan ta’addanci a Indiya.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *