kwangilar-pid-najeriya-za-ta-biya-dala-miliyan-200

Wata kotu a Birtaniya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta biya Dala miliyan 200 kafin kammala sauraron daukaka karar da ta yi kan hukuncin wata kotu wadda ta umurci kasar ta biya kamfanin P&ID diyyar sama da Dala biliyan 9 da rabi saboda saba yarjejeniyar kwangilar iskar gas.

Alkalin kotun da ke London, Christopher Butcher ya amince da dakatar da hukuncin kotun da ya mallaka wa kamfanin kadarorin Najeriya da suka zarce Dala biliyan 9 da rabi, yayin da ya umurci kasar ta biya Dala biliyan 200 cikin kwanaki 60.

Alkalin kotun ya ce, kamfanin P&ID na da hurumin kwace kadarorin Najeriya idan kasar ta gaza wajen biyan Dala miliyan 200 a cikin kwanaki 60 kamar yadda ya bada umurni.

Lauyan Najeriya, Harry Matovu ya ce hukuncin farko ya saba wa ‘yancin kasar, saboda haka suka bukaci soke hukuncin.

A shekarar 2012 ne gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejeniya da kamfanin da ke aikin samar da iskar gas, amma kuma aka gaza wajen aiwatar da kwangilar.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *