Yanayin-lafiyar-shugaban-rediyo-da-talabijin-kamaru-da-ke-tsare-ya-tabarbare

Yanayin lafiyar tsohon shugaban rediyo da talabijin mallakin gwamnatin kasar Kamaru Amadou Vamoulke da ke tsare a gidan yari yau shekaru uku na ci gaba da tabarbarewa.

Vamoulke, wanda sau 21 kotu na dage sauraren shari’ar da ake yi masa bisa zargin kashe kudade ba a kan ka’ida ba, kungiyar kare ‘yan jaridu RSF ta ce akwai bukatar bayar da dama domin duba lafiyarsa.

Kungiyar mai zaman kanta ta ce tana da rahoto kan lafiyar wanda ake zargin da ke nuni da cewa yana matukar bukatar a duba lafiyarsa.

A shekarar 2005 aka nada Amadou Vamoulké a matsayin shugana gidajen rediyo datalabijin na Kamaru, kuma a watan Yulin shekarar 2016 aka kama, yana kan mukamin na sa.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *