‘Yan sanda sun kame wadanda suka tone gawar DJ Arafat

‘Yan Sanda a kasar Cote d’Ivoire sun kama wasu mutane 12 da ake zargi da hannu wajen tone kabari tare da fasa akwatin gawar fitaccen mawakin kasar DJ Arafat domin daukar hotan sa.

Rahotanni sun ce lamarin ya afku ne ranar asabar bayan jana’izar da aka yiwa mawakin wanda ya samu daruruwan mutane a filin wasan kwallon kafar Abidjan.

Mai gabatar da kara Richard Adou ya ce sun kame mutanen 12 kuma tuni suka kaddamar da bincike akai.

Dj Arafat wanda ya yi suna sakamakon salon rawa da waka da ake yiwa taken coupé-décalé, yana da dimbim magoya baya a kasashen duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa lokuta kalilan bayan isar da akwatin gawar Arafat makabarta ne, magoya bayan na sa suka fitar da akwatin inda suka fasata don tabbatar da cewa fitaccen mawakin ne a cikin sa.

Da dama daga cikin magoya bayan matashin dan wasan dai kawo yanzu basu amince da cewa shi ne ya mutu ba.

A shekarar 1986 aka Dj Arafat wanda cikakken sunansa shi ne Ange Didier Huon.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *