Taliban ta dauki alhakin harin da ya hallaka mutane 16 a Kabul

Gwamnatin kasar Afghanistan ta ce mutane 16 aka tabbatar da mutuwar su, yayinda wasu sama da 119 suka samu raunuka sakamakon wani kazamin hari da mayakan kungiyar Taliban suka kai a cikin wata taraktan noma shake da bama bamai.PlayCurrent Time0:00/Duration Time0:04Loaded: 0%Progress: 0%0:00Fullscreen00:00Mute

Shidai wannan kazamin harin da aka kai birnin Kabul na kasar Afghanistan na zuwa ne kasa da sa’oi bayan da Jakadan Amurka na musamman Zalmay Khalilzad ya gana da shugaba Ashraf Ghani, inda ya gabatar masa da daftarin tatatunawar zaman lafiyar da su ke cigaba da yi da kungiyar Taliban da zummar ganin ta aje makaman ta.

Mai magana da yawun ma’aikatar cikin gida, Nasrat Rahimi ya tabbatar da mutuwar mutanen 16 daukacin su fararen hula, yayin da 119 suka samu raunuka daban daban a harin da aka kai unguwar da ke dauke da kungiyoyin agaji na kasashen duniya.

Rahotanni sun ce an ji karar harbe harbe da bindiga bayan kai harin, yayin da wani gidan mai ya kama da wuta.

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya sanar da kai jerin hare haren kunar bakin wake da na ‘yan bindiga.

Jakadan Amurka na musamman ya ce idan an fara aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da Taliban, Amurka zata janye dakarun ta daga sansanoni 5 cikin kwanaki 135, yayin da shugaba Donald Trump yace zasu bar sojoji 8,600 cikin kasar.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *