An fara yakin neman zabe a Tunisiya

Daga cikin ‘yan takara 24 da suka hada da mata biyu da ke neman mulkin kasar, har da Firai Ministan mai ci da kuma wani da aka tsare cikin watan jiya bisa zargin kauce wa biyan haraji da ma halalta wasu kudade na haram.

A ranar 15 ga wannan watan ne dai ake sa ran gudanar da zaben a Tunisiya, kasar da ta fuskanci juyin juya hali a shekara ta 2011.

Zaben dai ya biyo bayan mutuwar marigayi Shugaba Beji Essebsi ne a farkon watan Yulin da ya gabata, shugaba na farko a tsarin dimukuradiyya da ya hambare Shugaba Zine El-Abidine Ben Ali. 

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *