Ambaliyar ruwan sama ta kashe mutane 12 a Najeriya

Mutane guda 12 suka mutu a sakamakon ambaliyar a cikin Jihohin Jigawa da Yobe da Kano da Borno. Ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya tun daga ranar 20 zuwa 25 ga watan Augusta ya yi sanadin lallata hanyoyin da gidaje kana ya tilasta wa iyalai sama da dubbu goma yin kaura. A Borno cibiyoyin ‘yan gudun hijira da dama ruwan saman ya cisu inda jama’a suke cikin matsalar karancin cimmaka da ruwan sha da kuma magunguna.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *