Mali: Mautane 15 Ne Suka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Ruftawar wani Gini

Akalla mutane 15 aka tabbatar da sun rasa rayukansu sanadiyyar ruftawar wani gini da ba a kammala ba a kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, wani gini ya rufta a jiya a birnin Bamako fadar mulkin kasar, wanda ba a kammala gininsa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15 tare da jikkatar wasu da dama.

Ma’aikatar kula da harkokin tsaron cikin gida da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Mali sun sanar da cewa, lamarin ya faru ne da kimanin karfe 4 na yammacin jiya, amma a bayyana dalilin faruwar hakan ba.

Bayanin ya kara da cewa ginin mai hawa uku ya rufta ne a kan masu aiki da kuma gidaje makwafta, inda aka samu nasarar fitar da wasu daga cikin buraguzai, yayin da kuma wasu suka rasa rayukansu.

Ministan tsaro da kuma ministan ma’aikatar bayar da agajin gaggawa ta kasar tare da wasu manyan jami’an jami’an gwamnati sun isa wurin, domin tabbatar da cewa an gudanar da aikin ceto cikin gaggawa.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *