Kenya: An Gudanar Da Taron Tallafa Wa ‘Yan Gudun Hijra

An Kaddamar da wani taro domin tallafa wa ‘yan gudun hijra a kasar Kenya.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da taro inda gabatar da wani fim domin tara kudade na taimakawa ‘yan gudun hijra a kasar Kenya, kuma za a ci gaba da nuna fim din wanda Reza Meheranfar dan kasar Iran ya shirya har zuwa 6 ga watan Satumba a birnin Nairobi babban birnin kasar ta kenya.

Kafin kasar ta Kenya dai, an nuna wannan fim din a kasashen Amurka da Indiya da Faransa da Rasha.

Shi dai wannan fim, an shirya shi ne kan labarin wani yaro dan gudun hijra wanda yake cike da far gaba da tsoro.

Wadanda suka shirya taron sun ce an shirya wannan fim ne da nufin tabbatar da alaka tsakanin yara da matasa ‘yan gudun hijra, da kuma isar da muryoyinsu ga duniya, kuma kudin da aka tara za a taimakawa ‘yan gudun hijra da su.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *