Boko Haram: Sojojin Najeriya sun yi galaba a fafatawa

Rundunar sojojin Najeriya ta ce rundunarta ta Operation Lafiya Dole ta yi wa mayakan kungiyar Boko Haram « mahangurba » a yayin wani rangadi bayan da suka yi arba da su a yankin da ya hada Monguno da Mairari da Gajiram na jihar Borno.

A wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun rundunar Kanar Sagir Musa ya ce sojojin sun kashe da dama daga ‘yan kungiyar yayin da wasu kuma suka tsere da raunuka a ranar Juma’a.

« Sai dai uku daga cikin dakarunmu sun rasa ransu wasu takwas kuma suka samu raunuka. Ana ci gaba da kula da wadanda suka samu raunukan, » in ji Sagir Musa.

Ya kara da cewa rundunar ta kwace makamai masu yawa kuma har yanzu tana ci gaba da sintiri a yankin domin kakkabe ‘yan Boko Haram.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *