Bayan kashe mutum 16 an sa dokar ta-baci a Sudan

Gwamnatin rikon-kwarya ta Sudan ta kafa dokar-ta-baci a yankin gabashin kasar, bayan wani rikicin kabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 16.

Haka kuma gwamnatin ta wucin-gadi ta kori gwamnan jihar Red Sea, tare da babban jami’in tsaro na yankin.

Ba a dai san ainahin abin da ya haddasa rikicin ba, zuwa yanzu.

Wata sanarwa ta gwamnati ta ce a karon farko a irin wannan rikici, an yi amafani da bundugogi, abin da ke nuna alamun sanya hannun wasu na ciki da wajen kasar domin rura wutar rikicin.

A ‘yan kwanakin nan ne dai Sudan din ta fito daga rikici na wata da watanni,

inda aka yi yarjejeniyar kafa gwamnatin riko ta raba iko tsakanin farar-hula da soji, bayan kawar da gwamnatin dadadden shugaban kasar Omar al-Bashir.

Daga cikin muhimman ayyukan da ya fara sabon Firaministan kasar ya ce ya fara tattaunawa da Asusun Lamuni na Duniya IMF, da Bankin Duniya a wani yunkuri na sake fasali ga dimbin bashin da ake bin Sudan din.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *