Fashewar tankar mai da ya Afku a ranar Asabar data gabata kasar Tanzania ta yi sanadiyar mutuwar Mutane 69 tare da raunata mutun 70.

Hakan Ya kai ga shugaban Kasar Tanzania John Magufuli ya sanar da makokin kwanaki 3 a fadin Kasar.

Cikin Wani jawabi da firaiministar Kasar Kassim Majaliwa ya yi yace cikon na 69 ya rasu ne a yayin da aka dauke dashi da gaggawa cikin jirgi mai saukan angulu zuwa Babban asibiti dake Dar -es Salaam.

Wadanda sukaji rauni kuma sun kai mutune 66 da suke karkashin kulawarsu.

A cewar wasu shedun gani da ido yadda hatsarin ya Afku sunce tankar din ta fadi ne a yayin da take kokarin kauce ma wani babura inda daga bisani mutanen kauyen dama na kewaye sukayi cicirindo domin kwasan mai fetur da ya ke zubuwa daga tankar, daga nan ne gobara ta tashi.

A kiyasin karshe da gwamnan jahar Morogoro Stephen Kebwe ya bayyana a ranar Asabar data gabata ya ce Mutane 64 ne suka kwanta dama, 70 kuma suka ji rauni.

Al’amarin ya faru ne ranar Asabar a kwauyen Msamvu dake karkashin jahar Morogoro meda tazarar kilomita 200 da yammacin babban birnin cinikayyar Kasar.

Makammacin Wannan hatsarin ya taba afkua a Sudan ta kudu a shekarar 2015 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 203.
Sai kuma a Jamhuriyar Democradiyar Congo a shekara ta 2010 Inda ya kashe mutane 292.

Rahoto: Rabi Hassan Bachir

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *