Cuncoson ababen hawa a Douala ya jefa matafiya cikin halin hau’ila’i

sama da wata guda kenan da cunkoson ababen hawa ya zama ruwan dare gama gari a birnin cinikayyar kasar kamaru Douala, sakamakon aikin gyare gyaren hanyoyi da ke gudana a mashigar gabashin birnin.
Ga mahukunta, sakamakon mumunar aiki ne da aka yi ne aka kasance cikin wannan halin damuwar. Matafiya, musamman ma wadanda suke amfani da ababen hawan zuwa Yaounde babban birnin kasar ne suka shiga cikin mahuyacin halin sakamakon cunkoson.
Mahukuntan, sun dauki matakin gaggawa domin bude wata hanyar ta daban mai da nisan kilometa 18, wanda zai taimaka wajen rage zirga-zirgar ababen hawan, kafin a kammala ayyukan.
Minista mai kula da ayyukan jama’a a kasar kamaru, Emmanuel Nganou Djoumessi, ya nuna bacin ran sa kan yadda ayyukan suke tafiyar haweniya, musamman ma a wannan lokacin damuna, kuma ministan ya bukaci a gyara kananar hanyoyi da zai rage cunkoson, duk da cewa, zasu yi kokarin gyara hanyoyin, kuma ya yi wa kamfanin da ta ci kwangilan gargadi a gaban jama’a cewa bai ji dadi ba kan yadda aikin yake wakana a lokacin damuna, mai kula da kamfanin ya ce za su dau mataki ganin cewa sun bude hanyoyin yadda baza a samu kuma irin wannan cunkoson ba ministan ya yi wadannan bayanai ne yayin da ya kai ziayarar gani da ido a Douala.
An kiyasta shi a sama da milian 56 na kudin Amurka wato biliyan 22 na CFA, kuma a na bukatar gama ayyukan cikin gaggawa sakamakon gasar kwallon kafa na cin kofin nahiyar Afrika CAN da zai gudana a shekara ta 2021.
Wanan al’amarin ya zo ne bayan wata guda da babban magajin garin yankin wouri Joseph Bertrand Mache, ya yi umurnin haramta jigirlar manyan motoci a wasu lokuta da aka kayyade, daga karfe 9 na yamma zuwa karfe 5 na safiya amma duk da hakan ba a mutunta wannan dokar.

Rahoto Maimounatou Youssouf

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *