Ba a sake gano wani mutum mai dauke da cutar Ebola a Congo Demokradiya ba

Shin, cutar Ebola na cikin karshen sa’o’inta a garin Goma babban birnin kasuwanci na gabashin Jamhuriyar Democradiyyar Congo?


Amma hukumar kiwon lafiya ta duniya OMS ta MDD, tana da kyakyawar fata, inda ta sanar ranar lahdiN data gabata cewa, fiye da mutane dubu 1300 dauke da cutar an yi musu allurar riga kafi, kuma a yanzu sun samu kaso 98 cikin dari na cimma ayyukan su, duk da cewa, tun ranar 2 ga wannan watan ba’a gano wani sabon barkewar cutar ba.


Garin Goma, na dauke da kimanin mutane milian 2 dake da iyaka da kasar Rwanda, cikin makonnin 2 da suka gabata garin ya shiga cikin mumunar hali yayin da aka fara gano cutar Ebola.


Sama da shekara guda kenan, cutar ta habbaka a gabashin kasar Congo, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 1800, wanan shine kiyasi na 2 mafi muni a duniya, bayan na Afirka ta yamma da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 11000, tsakanin shekara ta 2013 zuwa 2016.
Wannan allaurar riga kafin, ya bada zai ba da damar yaki da cutar a kasar.

Kana, sakamakon barkewar cutar Ebola a kasar, hukumomin Saudiyya sun hana maniyyata gudanar da aikin Hajji bana, kuma dole ne za su dau hakuri zuwa shekara mai zuwa.

Kasar Jamhuriyar Democradiyyar Congo da kasar Rwanda, sun hada gwiwa domin yakar cutar Ebola.

Rahoto Maimounatou Youssoufa

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *