An gano wata sabuwar rijiyar man fetur, mai suna « le gisement du Delta de la cuvette a arewacin kasar Congo Brazzaville mai tsahon kilomita 9.392 a cewar Kamfanin sarrafa man fetur na SARPD Oil da PEPA.

Kamfanonin man fetur 2 da suka hada da SARPD oil da PEPA Sun Sanar da gano wata sabuwar Rijiyar Man fetur a garin OYo Mahaifar shugaban Kasar Congo Brazzaville Denis Sassou Nguesso sunyi Wannan sanarwar ce a ranar Asabar a yayin Wani taro.

A cewar Kamfanonin 2, filin da aka gano man fetur din nada tsahon mita 9.392 na kuma dauke da Rijiyoyi 4 inda aka fara sarrafa ta farkon tun a Watan Maris wannan shekara.

Bisa bincike da a ka yi a cewar daracta mai kula da bangaren kasuwancin Kamfanin SARPD oil Mohamed Rahmani, rijiyar za ta iya samar da fiye da bilyan 1 na bututun man fetur.

A halin yanzu dai Kasar Congo na cikin manyan kasashen Afirka masu samar da Man fetur, asali ma ita ce ta 3 bayan Kasar Najeriya da Angola.

A cikin Wani faifain bidiyo da aka bayyana yayin taron Wanda ya samu halartan jami’an gwammanati, shugaban Kasar ya nuna farin cikinsa matuka da samuwar wannan rijiyar, ya kuma ce abin alfahari ne ga Kasar sa, kuma hakan ya biyo bayan sakamakon gwagwarmaya da suka kwashe tsawon lokaci suna yi tun a shekara ta 1980.

Ya kara da cewa inganta wutan lantarki itace rawan da Amfanin Man fetur din zata taka a Kasar.

Rahoto: Rabi Hassan Bachir

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *