A kasar Nijar kungiyar agaji ta Médecin sans frontière ta ajiye aikinta a birnin Maïne Soroa sakamakon rashin ingantattcen tsaro a yankin.

Kungiyar agaji ta médecin sans frontière ta sanar cewar za ta kaurace wa garin Maïne soroa dalilin rashin tsaro a yankin Diffa a kudu maso gabashin Nijar, kusa da najeriya inda kungiyar yan ta’adda ta Boko haram ta ke kai hare- hare.

Shugaban kungiyar agajin Abdoul Aziz Mohamed ya sanar a yanar gizon MDD cewar wani aikin bincike ya sa sun lura ba a cika sharuddan matsalar tsaro domin ci gaba da aiki a yankin Maïne ba.

Ranar 26 ga watan Aprilu da ta gabata sun kai hari a ofishin majalisar dinkin duniya a Maïne ya raunata mutun daya daga cikin ma’aikatan, kuma maharan sun lalata gidaje sa’annan suka kone motoci hudu kurmus.

Bayan kai farmakin da a kai wa kungiyar agajin sun dakatar da wasu ayyukan su a bangaren Maïne,sashen da ke da mutane sama da 200.000 inda kungiyar mai zaman kanta ta fara ayyukan ta a shekara ta 2017 .

Mr Mohamed ya sanar cewar ba za su iya kai kansu cikin hadari da rayuwar ma’aikatansu ba da yake ba samu damar ba su gano wadanda suke kai hare-haren ba.

Rahoto Maimouna Abdoulaye

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *