A kasar Libya an kashe jami’an MDD uku sakamakon harin ta’addanci, wasu takwas kuma sun dikkata.

A kalla jami’an majalisar Dinkin Duniya uku ne suka rasa rayukansu takwas kuma sun raunata ciki har da yaro sakamakon wani harin ta’addancin da aka kai a anguwar Al’houari da ke Benghazi yayin da suke kan hanyarsu.

A cewar majiyan ministan harkokin cikin gida Ibrahim Bouchnaf da shugaban tsaro na Benghazi Janar Adel Abdel Aziz sun tafi wurin da lamarin ya faru domin gani da ido inda aka kai harin bam, don duba matakan tsaro da za a sanya a garin.

An kafa gwamnati da ba ta da ba bisa ka’ida a gabashin kasar da take Goyon bayan Marshal Khalifa Haftar, Wanda ya ayyana Kansa a matsayin mai iko da gabashin kasar.

An kaddamar da harin ta’addancin ne ranar 4 ga watan Aprilu da ta gabata tare da kungiyar sa (ANL)

Harin ya zo ne kasa da wata guda bayan wani makamancin harin da aka taba kaiwa a Benghazi yayin jana’izar wani tsohon ofishin Libya inda ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda tare da raunata wasu guda takwas.

Rahoto Maimouna Abdoulaye  
Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *