An tarwasa masu zanga-zanga a Hong Kong

‘Yan sanda sun tarwasa masu masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a yankin Hong Kong tare da harba musu barkonon tsohuwa a wani filin jirgin kasa da ke yankin.

Hakan ya faru ne ganin yadda masu zanga zangar suka bijire wa haramcin zanga zangar da ‘yan sanda suka yi musu inda suka mamaye manyan tituna, duk kuwa da gargadin da ake yi musu. Zanga -zangar ta wannan makon ita ce karo na goma a jere. 

Shugabanin Hong kong na gargadi da cewa yankin zai sami kanshi a wani mumunan hali a bangaren tattalin arziki idan har zanga-zangar ba ta tsgaita ba.

A baya dai wani babban jami’in gwamnatin Chaina ya gargadi masu zanga zangar a Hong Kong da cewa za su sanya kafar wando daya amma zanga zangar na ci gaba da yin kamari.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *