An bude wuta a masallacin kasar Norway

‘Yan sanda a kasar Norway, sun ce wani dan bindiga dadi dauke da makamai, ya buda wuta kan masallata a kusa da Oslo babban birnin kasar.

Jami’an tsaron sun ce sun cafke dan bindigar wanda matashi ne dan shekaru 20 da haihuwa; dan kuma asalin kasar.

‘Yan sanda sun ce shi kadai ne ya kai harin wanda ya jikkata wani dattijo mai shekara 75.Shaidu sun ce ya buda wutan ne da bindigogi biyu da ya shiga da su masallacin da ke cikin wata cibiyar nazarin addinin Islama a wajen birnin na Oslo.

Daraktan masallacin ya ce an tsaurara matakan tsaro a cikin masallacin, bayan harin nan da wani dan bindiga ya kai a birnin Christchurch na kasar New Zealand a farkon wannan shekara inda ya kashe mutane 51.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *