Wasan hawan kaho a Damagaram, Jamhuriyar Nijar

media

A duk rana ta 29 ga watan Ramadan lokacin da ake gaf da sallar azumi diyan mahauta a birnin Damagaram na gudanar da wata dadaddar al’ada ta wasa da gawurtattun marika majiya karfi, wasan da ake kira hawan kaho.

Diyan mahauta na nuna bajinta da dubaru hade da asirin ladabtar da bajimin sa a gaban jama’a. Ana shirya wasan ne da hadin gwiwar fadar sarkin Damagaram inda ake bi gidan sarakuna da magabata da mahadar jama’a.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *