Mai yiwuwa Real Madrid ta bada ‘yan wasa 3 ta karbi Pogba

‘Yan wasan Real Madrid 3 na iya barin kungiyar a karshen wannan kaka zuwa Manchester United a wata yarjejeniyar musaya su da Paul Pogba na Manchester United.

Dan wasan, wanda ya lashe kofin Duniya da Faransa, yana cikin ‘yan wasan tsakiya da Real Madrid ke fatan kawowa Santiago Bernabeu da zarar kaka ta kare, tare da ‘yan wasa kamar su Christian Eriksen da Donny van de Beek.

Sai dai rahotanni da ke fitowa daga kasar Spain na nuni da cewa Real Madrid ta shirya tsaf wajen bayar da ‘yan wasanta su uku, Gareth Bale, James Rodriguez da mai tsaron gida Keylo Navas don ta karbo Pogba.

Har ila yau rahotannin na cewa shugaban Real Madrid, Florentina Perez yana so ya kauce wa biyan kudi kai tsaye don sayen Pogba, saboda haka a shirye yake ya bada ‘yan wasa ukun kan dan wasan tsakiyan mai shakaru 26.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *